Hebrews 1

Ɗan Yana da Fifiko a kan Malaʼiku

1A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokatai dabam dabam da kuma a hanyoyi iri iri, 2amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. 3Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4Ta haka yake da fifiko a kan malaʼiku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

5Gama ga wane daga cikin malaʼikun Allah ya taɓa cewa,

“Kai Ɗana ne;
yau na zama Uba a gare ka”
Zab 2.7
?
Ko kuwa,

“Zan zama Ubansa,
shi kuma zai zama Ɗana”
2 Sam 7.14; 1 Tar 17.13
?
6Haka kuma, saʼad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya, ya ce,

“Bari dukan malaʼikun Allah su yi masa sujada.”
7Da yake magana game da malaʼiku kuwa ya ce,

“Ya mai da malaʼikunsa iska,
bayinsa kuma harsunan wuta.”
Zab 104.4

8Amma game da Ɗan, ya ce,

“Kursiyinka, Ya Allah, zai kasance har abada abadin,
adalci kuma zai zama sandan mulkinka.
9Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;
saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka,
ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”
Zab 45.6, 7

10Ya kuma ce,

“Tun da farko, Ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya,
sammai kuma aikin hannuwanka ne.
11Su za su hallaka, amma kai kana nan;
dukansu za su tsufa kamar riga.
12Za ka naɗe su kamar mayafi,
kamar riga za su sauya.
Amma kai ba za ka canja ba,
shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
Zab 102.25-27

13Ga wane daga cikin malaʼiku Allah ya taɓa cewa,

“Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka”
Zab 110.1
?
14Ashe, dukan malaʼiku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Copyright information for HauSRK